1/4
Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW) screenshot 0
Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW) screenshot 1
Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW) screenshot 2
Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW) screenshot 3
Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW) Icon

Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW)

uyaapps
Trustable Ranking Icon可信任
1K+下载次数
6.5MB大小
Android Version Icon4.0.1 - 4.0.2+
Android版本
1.0(18-11-2020)最新版本
-
(0 评价)
Age ratingPEGI-3
下载
详情评价版本信息
1/4

Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW)介绍

Wannan application yana dauke da tarihi na Annabi Mohammead (S.W.A), wanda wani shahararen marubucin tarihi ya wallafashi da harshen larabci.Shine aka fassara shi zuwa harshen hausa domin amfanarwa ga al'umar Hausawa wadan da ke neman ilimi akan cikakken tarihin Manzon Allah (S.W.A).

Littafin ya kunshi gundarin rayuwar Manzon Allah tun daga kan haihuwar sa, da kuma irin gwagwarmayar da yasha kafin a fara saukar masa da wahayi. Littafin bai tsaya nan ba kadai, ya kara bamu asali da kuma tarihi na musulunci tun daga kan annabi na farko, wato annabi Adam (AS) zuwa sauran annabawa, a takaice shi dai wannan littafi yafi bada karfi akan kafuwar musulunci da kuma rayuwar Annabi Mohammad (S.A.W).

Ina fatan wannan application wanda akayi shi don saukin amfani zai zamo abin amfanarwa ga al'umar musulmi.

Don Allah idan har kaji dadin wannan application kayi kokari ka yadashi don wasu suma su amfana.


Takaitaccen tarihin manzon Allah SAW.


Manzo Muhammad Al-Habib ɗan ʿAbdullahi (Sallallahu ʿalaihi wa sallam).


Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muɗallabi ɗan Hashimi ɗan Abdu-Manafi ɗan Ƙusayyi ɗan Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam, (Harshen Larabci: Abūl-Qāsim Muḥammad ibn ʿAbd Allāh ibn ʿAbd al-Muṭṭalib ibn Hāshim ibn ˁAbd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa maɗaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam.


Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (Āminah) 'yar Wahbi ɗan Abdu-Manaf ɗan Zuhrata ɗan Kilabi (Radhi Allahu anha). Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.


Laqabinsa: Almusxafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur'ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al'ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni'ima da Arrahma da Al'abdu da Arra'uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad'da'i da sauransu.


Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi'ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash'hurin zance gun Ahlul Baiti (a.s), an ce, 12 ga watan da aka ambata. Wurin haihuwarsa: Makka. Aikoshi: An aiko shi a Makka 27 Rajab yana xan shekara arba'in.


Koyarwarsa: ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da 'yan'uwantaka da rangwame na gaba xaya ga wanda ya shiga musulunci, sa'annan ya kafa shari'a maxaukakiya da dokoki na adalci da ya karvo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karva daga gare shi.


Mu'ujizozinsa: Mu'ujizarsa madauwamiya ita ce Kur'ani amma waxanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.


Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a voye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma. Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi'ul Auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.


Yaqoqinsa: Allah ya yi wa Manzo izinin yaqar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi xauki ba daxi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar- Uhud- Al-khandak (Ahzab)- Khaibar- Hunaini.


Matansa: KHadija 'yar Khuwailid (a.s) ita ce matarsa ta farko, amma sauran su ne: Saudatu 'yar Zami'a da A'isha 'yar Abubakar da Gaziyya 'yar Dudan (Ummu Sharik) da Hafsa yar Umar da Ramla 'yar Abu Sufyan (Ummu Habibia) da Ummu Salama 'yar Abu Umayya da Zainab 'yar Jahash da Zainab 'yar Huzaima da Maimuna 'yar Al-Haris da Juwairiyya 'yar Al-Haris da Safiyya 'yar Huyayyi xan Akhdabl.


'Ya'yansa: 1-Abdullah 2-Al-Qasim 3-Ibrahim 4-Faxima (a.s) a wani qaulin da Zainab da Ruqayya da Ummu Kulsum.


Ammominsa: Tara ne, su 'ya'yan AbdulMuxallib ne: Al-haris da Zubair da Abu Xalib da Hamza da Al-Gaidak da Dirar Al-muqawwam da Abu Lahab da Abbas.


Ammominsa mata: Su shida ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Amima da Ummu Hakima da Barra da Atika da Safiyya da Arwa. Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirulmuminina Ali xan Abi Xalib (a.s) da Hasan xan Ali da Husain xan Ali da Aliyyu xan Husaini da Muhammad xan Ali da Ja'afar xan Muhammad da Musa xan Ja'afar da Ali xan Musa da Muhammad xan Ali da Ali xan Muhammad da Alhasan xan Ali da Muhammad xan Hasan Mahadi (a.s).


Ayi karatu lfy


Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW) - 版本1.0

(18-11-2020)
其他版本

还没有评论或评分!要留下第一条评论或评分,请

-
0 Reviews
5
4
3
2
1

Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW) - APK信息

APK版本: 1.0程序包: com.andromo.dev646242.app676679
Android兼容性: 4.0.1 - 4.0.2+ (Ice Cream Sandwich)
开发商:uyaapps权限:2
名称: Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW)大小: 6.5 MB下载次数: 332版本: 1.0发布日期: 2020-11-18 11:34:50最小屏幕: SMALL支持的CPU:
程序包ID: com.andromo.dev646242.app676679SHA1签名: E4:47:63:A6:69:EA:E7:06:12:1C:8F:C5:37:00:94:65:9A:31:0C:9B开发商 (CN): Andromo App组织 (O): "Andromo.com L本地 (L): 国家/地区 (C): CA州/市 (ST): MB程序包ID: com.andromo.dev646242.app676679SHA1签名: E4:47:63:A6:69:EA:E7:06:12:1C:8F:C5:37:00:94:65:9A:31:0C:9B开发商 (CN): Andromo App组织 (O): "Andromo.com L本地 (L): 国家/地区 (C): CA州/市 (ST): MB

Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW)的最新版本

1.0Trust Icon Versions
18/11/2020
332 下载次数6.5 MB 大小
下载